Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Bayt (AS) – ABNA – ya ruwaito cewa: Mamayar cikin sa'o'in da suka gabata na yau Talata ta kai hari da harsashin manyan bindigogi a arewacin filin Marjeyoun, haka kuma garin Al-Mansouri da gefen garuruwan Kounine - Ainatha daga wajen Baraachit sun fuskanci harbin manyan bindigogi na Isra'ila.
A gefen garin Al-Mansouri ma, mamayar ta harba makamai masu sauri, kuma motocin Isra'ila sun shiga yankin da tankoki a unguwar Al-Mashaa tsakanin Al-Mansouri da Majdal Zoun.
Haka kuma, wani ɗan ƙasa ya ji rauni sakamakon fashewar wani abu daga ragowar abinda Isra'ila ta harba a kusa da gidan marayu a gefen garin Choukin na gundumar Nabatieh.
Waɗannan hare-haren suna zuwa ne a cikin tsarin ci gaba da keta "yarjejeniyar dakatar da wuta" da Isra'ila ke yi, inda "sojojin" mamayar ke gudanar da ayyukan rushewa da lalata da shafewa cikin ƙauyukan kudancin, kuma suna harba makamai a wasu ƙauyuka da manyan bindigogi da hare-hare na jiragen yaƙi da marasa matuƙa.
Waɗannan hare-haren suna ci gaba ne duk da tattaunawa kai tsaye da hukumomin Lebanon suka yi da Y’an ta’addar mamayar Isra'ila cikin watannin da suka gabata da kuma cimma abin da ake kira "yarjejeniyar tsari." Wacce ta ke ba ta da wani anfani sai cutarwa ga aksar Lebaon da al’ummarta kuma hukumar ta kasa dakatar da hare-haren.
Ra'ayinka